Matsalar tsaro ta shafi sallar idi a Pilato

A Jihar Filaton Nijeriya, ana cece-kuce kan matakin da hukumomi a jihar suka dauka na hana gudanar da Sallar idi dake tafe a biyu daga cikin masallatan idi dake Jos babban birnin Jihar, wadanda ke yankunan da kirista suka fi rinjaye.

Hukumomin dai sun bayyana cewa sun dauki matakin ne domin kaucewa irin tashin hankalin da aka fuskanta lokacin karamar Salla kimanin watanni biyu da suka gabata, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Da ma jihar ta Filato ta dade tana fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa wadanda suka haifar da rarrabuwar unguwanni a birnin na Jos.