Saif al-Islam na shirin tserewa daga Libya, in ji ICC

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saif al-Islam

Kotun hukunta masu aikata manyan laifukan yaki ta duniya, ICC, ta ce tana ci gaba da samun bayanai da ke cewa Saiful-Islam Gaddafi na kokarin tserewa daga Libya.

Babban mai shigar da kara na kotun, Mr Luis Moreno Ocampo ya ce ya samu wadansu rahottani da ke cewa Saiful Islam na shirin tserewa daga Libya, tare da taimakon sojojin haya.

Ya ce Saif al-Islam na wasu yankunan sahara na kasar Nijar inda ya ke ci gaba da buya.

Sai dai ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su kama shi, sannan su mika shi ga kotun don ya fuskanci sharia'a game da laifukan da suka shafi yaki.