An kai hare haren bam a Borno, Nijeriya

'Yan kunar bakin wake sun kai wasu jerin hare hare guda hudu a birnin Maiduguri, inda hukumomi ke fafatawa da 'yan gwagwarmayar Islama ta Boko Haram.

Wani kakakin sojin Laftana Kanar, Mohammed Hassan ya ce 'yan kunar bakin wake biyu sun mutu a harin.

Wasu rahotannin daga Damaturu babban birnin Jihar Yobe ma na cewar an ji karar fashewar wasu abubuwa a cikin birnin, abun da ya firgita mutane suka yi ta shigewa gidajensu.

Haka kuma sun ce sojoji biyu sun mutu a sakamakon harin.

Kungiyar ta Boko Haram dai ta kai hare hare masu yawa a cikin 'yan watannin nan, hade da harin bam a ofishin Majalisar Dinkin Duniya a birnin Abuja, cikin watan Agusta, inda mutane fiye da ashirin suka mutu.