An kaiwa Kiristoci hari a Zonkwa, Kaduna

Wasu daga cikin mutanen da suka rasa muhallansu a rikicin Zankwa na farko

Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu yayinda goma sha daya suka samu raunuka a wani hari da bindigogi da aka kai kan wasu masu ibada a coci a garin Zankwa da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya.

Hukumomi sun ce harin ya auku ne a cikin daren Juma'a yayinda mutanen da aka hara suke aiwatar da ibadar dare.

Wani jami'in 'yan sanda a Kaduna ya shaida wa wakilinmu Nura Muhammad Ringim cewa, da dama daga cikin wadanda suka samu rauni daga harbin na cikin mawuyacin hali.

Mutane da yawa - da dama daga cikinsu Musulmi- ne suka rasa rayukansu a rikicin bayan zabe da ya shafi garin na Zankwa.

Jihar ta Kaduna na fama da rarrabuwar siyasa, kabilanci da kuma addini.

Gudun Hijira

Musulmi da dama ne aka tilasta wa barin gidajensu a watan Afrilun da ya gabata bayan rikicin da ya biyo bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasa.

Rahotanni na cewa har yanzu akwai mutane kimanin 3,000 da ke zaune a wani sansani dake Kaduna babban birnin jihar, bayan an kona gidajensu a rikicin da ya biyo bayan zabe da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane.

Kaduna tamkar wata karamar Najeriya ce, inda Musulmi suka fi yawa a arewaci, yayinda Kiristoci suka fi yawa a Kudanci.

A watan Aprilun da ya gabata, Patrick Ibrahim Yakowa ya zamanto Kirista na farko da ya hau kujerar gwamna a jihar bayan zabe.

Fiye da mutane 1,000 ne suka rasa rayukansu a makociyar jihar Pilato inda ake samun hare-haren ramuwar gayya tsakanin bangarori biyu da ba sa ga maciji da juna, can ma akwai rarrabuwar siyasa da addini.