Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Yaye a yankunan karkara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata yarinya da aka haifa a Najeriya

Yaye wani mataki ne na fara janye yaro daga shan nono ta hanyar koya masa cin wasu nau'in abincin domin ya saba dasu kafin lokacin da zai daina shan nono kwata kwata.

Hukumar lafiya ta Burtaniya NHS kuwa ta yi bayani ne da cewa, daga zarar an fara baiwa yaro wani nau'in abincin bayan nonon uwa, to an shiga matakin yaye kenan.

Inda ta kara da cewa wannan wani mahimmin matakin girma ne da yaro kan bi.

Sashen lafiya na BBC da hukumar NHS din dai sun yi bayani kan cewa shirye-shiryen yaye wato fara baiwa yaro abinci kafin watanni hudu da haihuwa abu ne da za'a bayyana da cewa ya yi matukar wuri, Idan kuma ya haura wata tara, to za'a iya cewa ya yi latti sosai.

Don haka fara baiwa yaro abincin daga akalla watanni shidan farko zai taimaka wajen gujewa duk wata matsala da ka iya biyo bayan yaye shi.

Matakan da ake bi kafin a daina baiwa yaro nono kwata-kwata, kan faro ne daga akalla watanni shida da haihuwar yaro.

Inda za'a fara sabunta masa abinci mai ruwa ruwa kamar irinsu kunu ko farau farau, da dai sauransu tare da tabbatar da cewa ana ci gaba da shayar da yaro kamar yadda ya kamata.

Bayan wani dan lokaci kuma za'a fara kara yawan abincin da ake baiwa jariri, tare kuma da ci gaba da sabunta masa irin abincin da ake ci a gida, da kadan-kadan ta yadda kafin ya kai shekara guda ya saba da dandano daban-daban.

Daga wannan lokacin ne kuma kamar yadda Sashen Lafiya na BBC da hukumar NHS suka yi bayani, za'a fara rage yawan nonon da yaro ke sha, tare da maye shi da karin abinci har ya zuwa lokacin da za'a janye nonon baki daya.

Sabo da abincin a wannan mataki na shirye shiryen yaye, kusan za'a ce ya fi adadin abincin da yaro zai ci mahimmanci.

Domin daga zarar yaro ya fara sabawa da abinci, kara yawan adadin da za'a dinga ba shi, ba zai kasance me wahala ba, sannan kuma uwa za ta samu saukin iya musanya masa abincin iri-iri da mutanen gida ke ci, har ya zo ya saba.