Sabon tsarin bada kwangila a kungiyar UEMOA

A jamhuriyar nijar yau ne aka kammala wani taron karawa juna ilmi na kwanaki 5 da kungiyar UEMOA ta shirya domin yin bayani a kan tsarinta na bayar da kwangiloli na gwamnati a cikin kasashe mambobinta.

Kwararrun masana ne kungiyar ta kira domin yin bayani a kan matakai da hanyoyin da kowane dan kwangila ya dace ya bi, idan yana son samun kwangila daga wajen wata gwamnatin mambar kungiyar ta UEMOA.

Yanzu haka kungiyar ta UEMOA ta samar da layin waya domin tuntubarta game da batun cin hancin da wani yaga anayi a tsakanin kasashe mambobinta.