Tubman ya janye daga zaben Laberiya

Dan takarar 'yan adawa a Liberia, Winston Tubman ya ce ba zai shiga takara a zaben shugaban kasar da za a gudanar zagaye na biyu ba cikin makon gobe.

Ya kamata ace shi zai fafata da shugabar kasar mai ci, Ellen Johnson-Sirleaf, wadda ta samu kimanin kashi arba'in da hudu cikin dari na kuri'un da aka kada a zageyn farko na zaben.

Da ma dai ya sha korafin cewa akwai alamun za a tafka magudi a zaben zagaye na biyu.