Kotu ta kori karar da PDP ta shigar a Zamfara

Kotun sauraron kararrakin zabe dake zama a Gusau babban birnin jihar Zamfara ta yi watsi da karar da jam'iyya mai mulkin Najeriya ta PDP reshen jahar ta shigar tana kalubalantar nasarar da jam'iyyar adawa ta ANPP ta yi a zaben gwamnan jihar.

Kotun dai ta ce masu karar sun kasa kawo hujojin da zasu tabbatar da zargin tafka magudi, da keta ka'idojin zabe da suka yi akan wadanda suke kara.

Sai dai jam'iyyar ta PDP ta ce ba ta gamsu da hukuncin ba.