Ba musulmi bane suka kai hare-hare - Shugaba Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya yace ya fasa halartar daurin auren dan uwansa saboda hare haren da aka kai a arewacin Najeriya

Shugaban Najeriiya Dr Goodluck Jonathan ya yi Allah wadai da harin da aka a garin na Damaturu, yana mai cewa wasu bata gari ne kawai, amma ba Musulmai ba.

Shugban Nijeriyar, ya maida maratani ga hare-haren bama-baman na arewa maso gabashin Nijeriya ne a wani bayani da kakakinsa ya yi. Shugaban na Nijeriya Dakta Goodluck Jonatahn, ya ce ya damu matuka da faruwar wannan lamari, musamman ganin ya faru ne a lokacin hidimomin Sallah, kuma ya ce ya fasa wata tafiya zuwa jiharsa ta Bayelsa, da ya shirya tun farko kuma a cewarsa, ba zai halarci daurin auren dan uwansa ba kenan. Shugaban na Nijeriya da ya yai Magana ta bakin kakakinsa Reuben Abati, ya bayyyana cewa suna jin ba hakikannin musulmi ne suka yi wannan aikin ba. To sai dai kuma shugaba Goodluck Jonathan yace gwamnatinsa ta dukufa domin ganin an hukunta wadanda suka kuduri aniyyar kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin Nijeriya. Hare-haren na garin Damaturu dai, sun shafi majami'u ne da kuma hedikwatar rundunar 'yandasan, inda kungiyar agaji ta Red Cross ta bayyana cewa mutane sittin da uku ne suka rasa rayukansu. Koda yake wasu majiyoyi na cewa adadin ya fi haka.

Matsalar tsatro a Nijeriya, na daya daga cikin manyan kalubalen da kasar ke fuskanta musammna a baya bayan, inda huklumomi kan sha alwashin hukunta masu hannu a haddasa matsalar ba tare da an ga hakan a zahiri ba kuma 'yan kasar na ci gaba da zama cikin fargaba a sabo da tabarbarewar tsaron, amma kuma suna fatan ganin karshenta.