Ana nuna damuwa akan matsalar tattalin arzikin Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters

Ana ci gaba da nuna damuwa cewa, matsalar tattalin arzikin da ta dabaibaye Turai, take kuma dab da durkusar da kasar Girka, ta kuma fara barazana ga kasar Italiya, wadda ita ce ta uku a karfin tattalin arziki, cikin kasashe masu amfani da kudin euro.

Fargabar da ake nunawa cewa kasar ta Italiya zata gaza biyan dimbin bashin da ake binta, ya sa ana tsawwalawa gwamnatin kudaden bashin da ta ke nema.

Matsin lambar da ake samu a yanzu, ta sa praminista Silvio Berlusconi fitowa ya yi watsi da kiran ya yi murabus.

A Girka har yanzu ana can ana kokarin kafa gwamnatin hadin kan kasa.