An tsaurara matakan tsaro a Najeriya

Hakkin mallakar hoto Reuters

An tsaurara matakan tsaro a babban birnin Najeriya, Abuja bayan wata sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a kasar ya fitar da ke cewa kungiyar Boko Haram na shirin kai hare hare akan manya-manyan otel-otel a birnin.

Wakilin BBC Abuja ya ce akwai karin jami'an tsaro na soji da 'yan sanda dake sintiri a titunan birnin.

Ana kuma binciken abubuwan hawa.

Sai dai kuma ma'aikatar harkokin wajen kasar ta yi kira ga jama'a a birnin dasu kwantar da hankalin su tana mai cewa kada sanarwar ta razana su

Fiye da mutane dari ne suka mutu a wasu hare hare da tashin bama bamai da aka kai a garin Damaturu a arewacin kasar a makon jiya