An kammala zaben Liberia

Masu zabe a Liberia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zabe a Liberia

An kammala kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben Shugaban kasar Liberia -- wani zagayen da dan takarar 'yan adawa, Winston Tubman ya janye daga takara. Ya yi ikirarin cewar zaben ba a yi shi cikin gaskiya da adalci ba.

A zagayen farko, Shugabar mai ci, Ellen Johnson-Sirleaf, na kan gaba da kashi kusan arba'in da hudu cikin dari.

Wani wakilin BBC a Monrovia babban birnin kasar, ya ce a wata rumfa daya a birnin, mutane takwas ne kawai suka jira su kada kuri'arsu, ba kamar daruruwa a watan da ya wuce ba.

Farfesa Attahiru Jega, Shugaban hukumar zabe ta Najeriya, daya daga cikin masu sa ido a zaben, ya shaidawa BBC cewar bai yi mamakin rashin fitowar jama'a da yawa ba, saboda 'yar takara guda ce, bayan janyewar dan adawar.