Yau za a kafa gwamnatin hadaka a Girka

Firayim Minista George Papandreou na Girka Hakkin mallakar hoto papandreou
Image caption Firayim Minista George Papandreou na Girka

Wani jami'in gwamnati a Girka ya ce nan gaba a yau Laraba za a bayar da sanarwar kafa wata gwamnatin hadin kan kasa wadda za ta dauki mataki a kan matsalar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Jami'in ya ce a yau din kuma, Firayim Minista George Papandreou, wanda tuni ya bayar da sanarwar zai yi murabus, zai ziyarci shugaban kasar.

Ranar Litinin ne dai aka fara tattaunawa a tsakanin shugabannin jam'iyyun kasar.

Rahotanni sun ce mai yiwuwa tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Turai, Lucas Papademos, ya zama firayim minista, to amma alamu na nuna cewa takararsa ta ci karo da matsala.

Kwamishina mai kula da tattalin arzikin Tarayyar Turai, Ollie Rehn, ya ce wajibi ne sabuwar gwamnatin da za a kafa ta jaddada kudurinta na aiwatar da yarjejeniyar ba kasar ta Girka tallafi a rubuce.

“Lallai kam, wajibi ne sabuwar gwamnatin ta fito karara, kuma a rubuce, ta bayyana kudirinta na aiwatar da shawarwarin da kasashe masu amfani da kudin euro goma sha bakwai suka yanke ranar 27 ga watan Oktoba” in ji Mista Rehn.