Wasu 'yan Hindu ne suka kashe Musulmai a India

Wata kotu a India ta samu wasu 'Yan Hindu 31 da laifi game da kona musulmai a lokacin wata tarzomar addini a jihar Gujarat shekaru 9 da suka wuce.

Musulmi 33 ne suka mutu bayan da suka hallara a wani gida a kauyen Sardarpura, suna dai neman tserewa ne daga masu tarzomar, wadanda daga nan suka cunna wa ginin wuta.

Duka duka dai mutane kusan dubu 2 ne suka mutu a lokacin tashin hankalin a Gujarat -- wanda wata gobara a wani jirgin kasa da ta kone wasu maziyartan ibadar Hindu da ransu, ta haddasa.