Iran ta mayar da martani ga rahoton IAEA

Ali Asghar Soltanieh
Image caption Jakadan Iran a hukumar IAEA, Ali Asghar Soltanieh

Iran ta mayar da martani mai zafi a kan rahoton da hukumar kula da makamshin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, IAEA, ta fitar, wanda ke cewa alamu sun nuna cewa kasar ta gudanar da wadansu ayyuka wadanda za su iya kaiwa ga kera makamin nukiliya.

Gwamnatin kasar ta Iran, wadda ta sha nanata cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne, ta yi Allah-wadai da rahoton, tana mai cewa an wallafa shi ne da wata manufa ta siyasa.

Jakadan kasar a hukumar ta IAEA, Ali Asghar Soltanieh, ya zargi shugaban hukumar da yin rawa da bazar tsohuwar gwamnatin Amurka.

A cewarsa, “wannan ne karo na farko a traihin IAEA da shugaban hukumar ya tafka irin wannan gagarumin kuskure, kuma za mu dora masa alhakin duk wani abin da ka iya biyo bayan kuskuren”.

Hukumar dai ba ta fito karara ta ce Iran na kera makamin nukiliya ba, amma rahoton ya ce wani bangare na binciken da kasar ke gudanarwa ya nuna alamun hakan.

Wani jami'in gwamnatin Amurka ya ce Washington za ta kara kaimi wajen kakabawa Iran din karin takunkumi.