Rasha ba za ta amince da takunkumi a kan Iran ba

Ma'aikatar nukiliyar Iran Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Akwai alamar Russia za ta hau kujerar na-ki

Rasha ta ce ba za ta amince da wani sabon takunkumi a kan Iran ba, bayan wallafa wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ke nuna sabuwar damuwa game da shirin Iran din na nukiliya ba.

Wani kakakin kasar ta Rasha ya ce mutane da yawa za su fassara sabon takunkumin a matsayin wani kokari na tilasta sauyin gwamnati a Iran.

Birtaniya da Faransa sun ce ya kamata a dubi yiwuwar daukar sababbin matakai a kan bangarorin kudi da mai da kuma Iskar gas na Iran.

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce rahoton ya tabbatar cewa dole ne duniya ta hana Iran abin da ya kira, neman kera makaman nukiliya.

Iran dai ta musanta duk wani buri na nukiliya domin soji.

Shugaba Mahmoud Ahmadinejad ya yi watsi da rahoton, sannan ya sake sukar da ya yi wa Hukumar Makamshin Nukiliyar ta IAEA, yana cewa ta rubuta rahoton nata ne cikin matsi daga Amurka.