Berlusconi ya ce zai yi murabus, amma...

Firayim Ministan Italiya, Silvio Berlusconi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Firayim Ministan Italiya, Silvio Berlusconi

Firaministan Italiya, Silvio Berlusconi, ya ce zai yi murabus, amma sai majalisar dokokin kasar ta amince da wani jerin sauye-sauyen karfafa tattalin arzikin kasar, wanda matsalar bashin da ta addabi kasashe masu amfani da kudin Euro ta shafa.

Ana dai sa ran gabatar da sauye-sauyen a gaban majalisar nan da makwanni biyu.

Wannan sanarwa ta Mista Berlusconi ta zo ne bayan da sakamakon wata kuri'a a majalisar ta nuna cewa rinjayen da ya ke da shi ya zaizaye.

Tuni dai kudin ruwa a kan takardun bashin gwamnatin Italiya ya yi kasa bayan ya yi tashin gwauron zabi, abin da ke nufin cewa kasar za ta samu saukin ciwo bashi a kasuwannin duniya.

Karin bayani