Kudin ruwan bashin Italiya ya karu

Kudin ruwan bashin da kasar Italiya ta ci ya karu ya zuwa wani matsayi na innanaha,kwana daya bayan Pirayim Ministan kasar, Silvio Berlusconi ya bayyana cewar ya shiryi yin murabus.

Kudin ruwan da kasar Italiya za ta biya ga takardun bashinta sun karu ya zuwa fiye da kashi 7 cikin dari - irin matsayin da sauran wakilan kasashe masu amfani da kudin Euro kamar irinsu Ireland da Portugal da kuma Girka suka kai ya sa su neman ceto.

Wani wakilin BBC kan harkokin kasuwanci ya ce, a halin yanzu akwai yiwuwa mai karfi cewar Italiya za ta bukaci rancen gaggawa -- to amma babu wadatattun kudi a asusun ceto na kasashe masu amfani da kudin Euro.

Da yake magana bayan wani taro na Ministocin kudin kungiyar Tarayyar Turai, Babban jami'in kula da harkokin tattalin arziki na kungiyar, Olli Rehn, ya ce dole ne a aiwatar da matakan daidaita lamura a Italiya nan ba da jimawa ba.

Inda ya ce, yanayin tattalin arziki da kudi na Italiya abun damuwa ne matuka, kuma muna son taimaka wa Italiya ta hanyar sa ido kwakwaf da muke yi.