Rikici ya barke a Kafanchan

Jahar Kaduna Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jahar Kaduna

Rahotanni daga Kafanchan a jihar Kaduna na cewa har yanzu ana zaman dar-dar sanadiyar rikicin da yi bayan da wasu wadanda ba a san ko su wanene ba suka hallaka wani dan Acaba Musulmi.

Bayanai sun nuna cewa 'yan sanda sun kama wasu Kiristoci bisa zarginsu da aikata kisan, abinda ya harzuka matsa kiristoci suka fara zanga-zanga wadda daga bisani ta haifar da dauki ba dadi tsakanin matasa Musulmi da Kirista a garin.

Hukumomi sun sanya dokar hana fitar dare a garin.

I zuwa yanzu dai babu bayanan jikkata ko rasa rayuka sakamakon zanga-zangar.