Shell ne ke da alhakin gurbatar muhalli a Bodo

Kungiyar kare hakkin Jama'a ta Amnesty International da Cibiyar kare muhalli da bil adama ta Centre for Environment, Human Rights and Development sun kaddamar da wani rahoto dake kira ga kamfanin mai na Shell da ya dauki alhakin gurbatar muhallin da ya janyo a yankin Naija Delta ta hanyar malalar mai.

Rahoton ya kuma nemi Shell da ya dauki nauyin fara aikin share dagwalon danyen man da ya janyo, wanda ya jefa dubban rayukan a cikin mawuyacin hali.

Sannan kuma rahoton ya kalubalanci gwamnatin Najeriya da kin daukar mataki.

Wannan kuma na zuwa ne a ranar tunawa da kisan mai fafutukar kare hakkin 'yan kabilar Ogoni nan, Ken Saro Wiwa.