ANC ta dakatar da Julius Malema na shekaru biyar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban matasan jam'iyyar ANC, Julius Malema, yana gangamin siyasa

Jam'iyya mai mulki a kasar Afrika ta kudu, ANC, ta samu shugaban matasan jam'iyyar, Julius Malema da laifin bata sunnan ta.

Jam'iyyar har wa yau ta dakatar da shi na tsawon shekaru biyar kuma ta tubuke shi daga mukaminshi na shugaban matasan jam'iyyar.

Malema , wanda a baya na kusa ne ga shugaba Jacob Zuma, ya zama daya daga cikin mutanen da suka fi sukar shugaban kasar, inda ya zargi shi da watsi da al'amuran talakawan kasar, bayan sun taimaka mishi ya hau karagar mulki a shekara ta 2009.

Wakilin BBC Milton Nkosi ya ce hukuncin da jam'iyyar ANC ta yanke a kan Malema, zai taimakawa yankin neman zaben Mista Zuma.

Mista Malema dai na neman ne a sauya Mista Zuma a matsayin shugaban jam'iyyar, kafin a shirya zaben shekara ta 2014.

Jam'iyyar dai za ta yi bikin cika shekaru 100 a watan Junairun shekara ta 2012.

Jam'iyyar dai ta dakatar da shine, bayan ya nemi a sauya gwamnati a kasar Botswana, abun da kuma ya keta tsarin jam'iyya da gwamnatin kasar.

Karin bayani