Ana jiran sakamakon zabe a Liberia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana kidaya kuri'u har cikin dare, amma jama'a da dama sun kauracewa zaben.

A yau Alhamis ne ake sa ran fara samun sakamakon farko na zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Liberia.

Ana kyautata zaton shugaba mai ci, Ellen Johnson Sirleaf, ita ce za ta lashe zaben bayan abokin hamayyarta, Winston Tubman, magoya bayansa sun kauracewa zaben.

Mr Tubman dai ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben da aka gudanar a zagaye na farko.

Jama'a basu fito sosai a zaben zagaye na biyu ba, kuma wakilin BBC a yammacin Afrika ya ce, rashin rinjaye a majalisar dokoki ka iya yin illa ga shugabancin Mrs Sirleaf karo na biyu.

Dan takarar 'yan adawa Winston Tubman dai ya kauracewa zaben, yana mai cewa ba a cika sharuddan gudanar da sahihin zabe ba.

A ranar jajibirin zaben zagaye na biyu sai da aka bindige akalla mutum guda a Monrovia, babban birnin kasar, yayin wani gangami na 'yan adawa.

A lokacin dai da mataimakin shugaban 'yan adawar, tsohon dan wasan kwallon kafa George Weah ya yi kira a dage zaben, yana mai cewa:

"Muna cikin wani gangami na lumana dauke da kyallaye da kwalaye masu dauke da sakon a yi adalci, a bi hanyar tabbatar da dimokuradiyya, sai kwatsam aka fara jefo mana hayaki mai sa hawaye".

Karin bayani