Yau ake sa ran fitar da sakamakon zaben Liberia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mutum na kada kuri'arsa a lokacin zaben Liberia

A yau Alhamis ne ake sa ran fara samun sakamakon farko na zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Liberia.

Ana kyautata zaton shugaba mai ci, Ellen Johnson Sirleaf, ita ce za ta lashe zaben bayan abokin hamayyarta, Winston Tubman, magoya bayansa sun kauracewa zaben.

Mr Tubman dai ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben da aka gudanar a zagaye na farko.

Jama'a basu fito sosai a zaben zagaye na biyu ba, kuma wakilin BBC a yammacin Afrika ya ce, rashin rinjaye a majalisar dokoki ka iya yin illa ga shugabancin Mrs Sirleaf karo na biyu.