Mutane biyu sun mutu a kusa da Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Motocin jami'an tsaro da aka kona a garin Damaturu a karshen mako

A Najeriya, rahotanni daga garin Mainok kusa da Maiduguri da ke jihar Barno sun ce akalla mutane biyu sun mutu bayan wasu da ba a san ko su waye ba, sun kai hari a kan ofisoshin 'yan sanda da na hukumar kiyaye hadura da ke garin.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce a daren jiya Laraba ne mutanen suka bude wuta a ofisoshin kuma wuta ta cinye su.

Kakakin rundunar tabbatar da tsaro ta hadin gwiwa JTF, Laftanal Kanal Hassan Mohammed , ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ya ce ba zai yi karin bayani ba har sai sun kammala tattara bayanai game da batun.

Jihar Barno dai ta sha fama da hare-hare wadanda ake zargin 'yan kungiyar Ahlussunna Lidda'awati Wal jihad, wadda aka fa sani da Boko Haram da kaiwa.

A ranar juma'ar da ta gabata mai, sai da aka kaddamar da wasu hare-hare a garin Damaturu a jihar Yobe, inda ya yi asarar rayuka sama da sittin.

Tuni dai Hukumar 'yan sanda a kasar ta ce ta kama wasu mutane da take zargi suna da hannu a lamarin.

Karin bayani