An bukaci kamfanin Shell ya biya diyya

Image caption Cibiyar hakar mai ta Shell

Kungiyar kare hakkin bil adama ta duniya, Amnesty International, ta yi kira ga kamfanin hakar mai na Shell da ya fara biyan diyyar dala biliyan daya ga al'ummomin garin Bodo, da ke yankin Naija Delta na Najeriya.

Kungiyar dai ta yi wannan tsokaci ne, tare da hadin gwiwar Cibiyar Kula da Muhalli da kuma kare hakkin dan Adam da ke yankin na Naija Delta.

Malalar man da aka samu a Bodo a shekara ta 2008 ta yi sanadiyar mutuwar kifaye tare da lalata gonaki, abin da ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki a yankin.

Najeriya dai na da arzikin mai, sai dai hakarsa na gurbata muhalli, abin da mazauna yankunan da ke da shi ke cewa na yin barazana ga rayuwarsu.

Kamfanin mai na Shell ya amince da cewa shi ne ke da alhakin kwararar mai manya-manya guda biyu a yankin Naija Delta.

BBC ta ga wata wasika daga kamfanin Shell din inda kamfanin ya amince da daukar nauyin wannan kwarar mai.

A farkon wannan shekara ma, sai da wata kotu a Burtaniya ta bukaci, kamfanin na Shell ya biya diyya ga wasu al'umomin Niger Delta da aka gurbatawa Muhalli.

Al'umomin yankin Niger Delta dai na fuskatar talauci duk da arzikin man fetur da yankin ke da shi.

A baya an samu masu fafutukar ikirarin kwato 'yan cin yankin, wanda su ke kai hare-hare akan batutun mai, wanda shima kan gurbata muhalli.

Karin bayani