Italiya ta amince da shirin tsuke aljihu

Mario Monti yana isa majalisar dattawan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mario Monti , tsohon jami'in EU, yana isa majalisar dattawan

Majalisar dattawan Italiya ta amince da kudirin matakan tsuke bakin aljuhun gwamnatin kasar wanda aka yi tan jinkirin amincewa da shi.

Mataimakiyar shugaban majalisar dattawan kasar Rosa Angela Mauro ce ta bayyana amincewa da matakin.

Ana sa ran majalisar wakilan kasar zata bada amincewar karshe ga shirin a karshen mako.

Shirin dai wani mataki ne na kawo karshen matsalar bashin da ta addabi kasar dama, a sauran kasashen Turai.

Amincewar majalisar wakilan kasar zata kai ga murubus din Praministan Minista Silvio Berlusconi.

Karin bayani