BBC navigation

Italiya ta amince da shirin tsuke aljihu

An sabunta: 11 ga Nuwamba, 2011 - An wallafa a 16:04 GMT
Mario Monti yana isa majalisar dattawan

Mario Monti , tsohon jami'in EU, yana isa majalisar dattawan

Majalisar dattawan Italiya ta amince da kudirin matakan tsuke bakin aljuhun gwamnatin kasar wanda aka yi tan jinkirin amincewa da shi.

Mataimakiyar shugaban majalisar dattawan kasar Rosa Angela Mauro ce ta bayyana amincewa da matakin.

Ana sa ran majalisar wakilan kasar zata bada amincewar karshe ga shirin a karshen mako.

Shirin dai wani mataki ne na kawo karshen matsalar bashin da ta addabi kasar dama, a sauran kasashen Turai.

Amincewar majalisar wakilan kasar zata kai ga murubus din Praministan Minista Silvio Berlusconi.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.