An samu fashewar nakiya a Bauchi

Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa mutane biyar sun jikkata, a sakamakon fashewar wata nakiya.

Lamarin ya auku ne a unguwar Wutin Dada, kuma rundunar 'yan sandan jihar ta Bauchi ta ce tana gudanar da bincike.

Nijeriya dai na ci gaba da fuskantar tabarbarewar tsaro, musamman a baya-bayan nan, duk da matakan da hukumomi ke cewa suna dauka.