Faransa zata taimakawa Najeriya ta fuskar tsaro

Ministan harkokin wajen Faransa, Alain Juppe, yace kasarsa zata taimakawa Najeriya wajen yaki da kungiyoyi masu tsautsauran ra'ayi.

Alain Juppe ya bayyana hakan ne, a ziyarar da ya kai Najeriya a yau, bayan ya gana da takwaran aikinsa na kasar, Olugbenga Ashiru.

A cewar ministan harkokin wajen Faransar, kasarsa ta damu matuka game da karuwar ayyukan ta'addanci a yankin Sahel, don haka ne ma za su taimakawa kasashen yankin, domin tinkarar matsalar.