Mutane fiye da goma sun mutu a Zamfara

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

Hukumomin 'yan sanda a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane goma sha hudu da raunatar wasu mutane biyar sakamakon wani kazamin hatsarin mota a jahar Zamfara a jiya Juma'a.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce hatsarin ya auku ne tsakanin wata karamar mota, da kuma wata bos a wani waje da ake gyaran hanya daf da kauyen Wanzamai da ke kan iyakar jihar da jihar Katsina.

Sun ce galibin wadanda suka mutu sun kone kurmus kuma wani mazaunin yankin da lamarin ya auku ya ce wadanda suka mutu a hatsarin sun kai talatin.

Hatsarin mota dai na yawan faruwa a Najeriya, akasari sakamakon tukin ganganci da kuma mummunan yanayin da hanyoyin kasar ke ciki.

Karin bayani