Ana jiran Mr. Berlusconi ya yi murabus

Silvio Berlusconi, pira ministan Italiya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Silvio Berlusconi, pira ministan Italiya

Majalisar wakilan kasar Italiya ta amince da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati, a wani yunkuri na kokarin kwantar da hankalin kasashe game da cewa, tana iya biyan dimbin bashin da ake binta.

Nan ba da jimawa ba kuma ana sa ran Praministan Italiyar, Silvio Berlusconi, zai yi murabus, ya mika iko ga gwamnatin rikon kwarya.

Praministan dai yayi alkawarin zai sauka daga mulki, da zarar majalisar wakilan ta amince da matakan rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa, wadanda tuni majalisar dattawa ta yi na'am da su.

Tsohon kwamishinan Tarayyar Turai, Mario Monti, shine ake jin zai maye gurbin Silvio Berlusconi.

To amma kuma in ji wakilin BBC a birnin Rome, yana fuskantar jar adawa daga gwamnatin hadin gambiza mai barin gado.

Karin bayani