Ana samun baraka tsakanin bangorori a Libya

A Libiya akalla mayaka biyu sun hallaka a yammacin kasar, a wani fada tsakanin 'yan bindigar da ba sa ga maciji da juna.

Daya daga cikin bangarorin biyu ya zargi abokan hamayyarsa da cewa, sun goyi bayan tsohon jagoran kasar, marigayi Muamman Gaddafi.

Yayin da daya bangaren ya ce, an yi taho-mu-gamar ne akan batun mallakar wani sansanin soja.

A Libiyar dai, mayakan sa-kan da suka yaki tsohuwar gwamnatin Gaddafi, suna da ikon fada-a-ji a yankunan kasar da dama, yayin da sabuwar gwamnati ke ta kici-kicin tsarawa da kuma hada kan dakarun tsaron kasar.