An azabtar da masu zanga zanga a Khartoum

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, ta zargi gwamnatin Sudan da gallazawa masu gwagwarmaya na bangaren adawa, wadanda suka shiga jerin zanga zangar da aka yi a baya bayan nan.

A cewar Amnestyn, a watan Oktoban da ya wuce, an kama mutane fiye da dari a ciki da kewayen birnin Khartoum, bayan zanga zangar da aka yi akan hauhawar farashin kayan masarufi.

Dayawa daga cikin wadanda aka kaman sun ce an azabtar da su, ta hanyar dukansu, da harbin su da kafa, da kuma hana su barci.

Kawo yanzu dai hukumomin Sudan din basu mayar da murtani ba game da zarge zargen.

Karin bayani