An dakatar da Syria daga kungiyar Larabawa

Taron kungiyar kasashen Larabawa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Taron kungiyar kasashen Larabawa

Kungiyar kasashen Larabawa ta dakatar da kasar Syria daga shiga duk wasu aikace-aikacenta, har sai lokacin da Syrian ta aiwatar da yarjajeniyar kawo zaman lafiyar da bangarorin biyu suka cimmawa, a makon jiya.

Kungiyar ta kuma sa wa gwamnatin Syrian takunkumin karya mata tattalin arziki, sannan ta bukaci mambobinta da su janye jakadun su daga kasar ta Syria.

A cikin sanarwar da aka bayar, bayan taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen Larabawan a birnin Alkahira, an yi kira ga rundunar sojan Syria da ta daina kaiwa masu zanga zanga hari.

Wakilin BBC ya ce, ko kasashen larabawan da ba sa kaunar masu zanga zangar sun soma fahimtar cewa, ba zasu iya yin biris da halin da ake ciki a Syria ba.

Karin bayani