An kashe dan fashin ruwa a Turkiyya

An kashe dan fashin ruwa a Turkiyya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar PKK ta dade tana yakar gwamnatin Turkiyya

Jami'an tsaron Turkiyya sun harbe har lahira wani mutum da ya yi fashin wani karamin jirgin ruwa a kusa da gabar ruwan Santanbul ranar Juma'a.

Jami'ai sun ce babu wanda ya samu rauni a cikin fasinjoji 24 da kuma matukin jirgin, sai dai wasu rahotanni sun ce wasu daga cikinsu sun fada cikin ruwa bayan fara sumamen sojin.

Har yanzu dai jami'an na Turkiyya na kokarin gano maharin, wanda suka ce yana dauke da wasu abubuwa masu fashewa a jikinsa.

Wakilin BBC a Turkiyya ya ce Jami'ai sun bayyana shi da cewa mamba ne a wata kungiyar 'yan ta'adda - abinda ke nufin kungiyar 'yan tawaye ta Kurdawa PKK, wacce ta shafe shekaru kusan 30 tana yakar gwamnatin Turkiyyar.

Kafafen yada Turkiyya dai sun ce sojoji sun kai farmaki kan karamin jirgin ruwan da jijjifi, inda suka harbe dan fashin tekun da ya kwace shi, kuma nan take ya mutu.

Babu isasshen mai a jirgin

Ministan zirga-zirga na Turkiyya, Binali Yildirim, ya ce mai ya kusa karewa jirgin a lokacin da yake dab da isa birnin Santanbul.

Sai dai ya ce gwamnati na baiwa tsaron lafiyar mutanen da ke cikin jirgin ruwa muhimmanci:

"Jirgin ya doshi tsibirin Selimpasa da ke kusa da Santambul. Kuma a lokacin ne mai ya kusa kare masa.

Haka kuma mutanen da ke cikinsa na bukatar abinci, an kuma shiada wa matukin jirgin bukatarsu. Amma dai abu mafi muhimmanci shi ne matuka jirgin da fasinjojin basu samu raunuka ba".

Ya kara da cewa za su tabbatar da tsaron lafiyar mutanen.

A halin yanzu dai, jami'ai a kasar na kokarin gane gawar dan fashin tekun, wanda rahotanni suka ce yana dauke ne da abubuwan da ke fashewa a lokacin da ya shiga jirgnin.

Sai dai wasu jami'an na cewa, dan fashin mamba ne na kungiyar Kurdawa, masu tayar da kayar baya, mai suna PKK.

Karin bayani