ACN: Yakamata aji ra'ayin jama'ar kasa

A Najeriya, jam'iyyar adawa ta ACN ta yi kira da a gudanar da zaben raba gardama, a kan batun cire tallafin man fetur, da kuma batun kara wa'adin mulki zuwa shekara 6 da gwamnatin tarraya ke son a yi.

Jam'iyyar ta ACN ta ce, ya kamata a gabatar wa 'yan kasar wadannan batutuwan, domin jin ra'ayinsu.

A yanzu haka dai ana ta takaddama a Najeriyar, a kan batun cire tallafin da gwamnati ke baiwa bangaren mai.

A farkon shekara mai zuwa ce ta 2012 gwamnatin Najeriyar ta ce za ta daina bada tallafi ga harkokin mai a kasar.

Gwamnatin ta kare matakin da cewa, a yanzu tallafin da take bayarwa ba ya kaiwa ga talakawa.