Amurka na da muradi a yankin Asiya da Pacific

Shugaban Amurka Barack Obama Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Amurka zata kara yawan sojojinta a yankin Asiya da Pacific

Shugaba Obama ya ce Amurka na da niyyar taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar yankin Asiya da Pacific saboda muhimmancin yankin ga muradun Amurka.

Mista Obama ya kuma ce rage kashe kudaden Amurka a kan al'amuran soji ba zai tauye karfin Amurka na fada-a-ji a yankin ba.

Shugaban ya ce yankin Asiya da Pacific shine inda Amurkar ta fi baiwa fifiko dangane da manufofinta na harkokin Kasashen waje.

Shugaba Obama ya kara da cewar za a ware kudaden da ake bukata domin kara yawan sojojin Amurka a wannan yanki.

Dangane da Kasar China kuwa, Shugaban yace Amurka ta lura da yadda Kasar ke habbaka amma ya ce dole ne Chinan ta bi ka'idojin Kasa da Kasa.

Karin bayani