'Boko Haram na da alaka da al Qaeda'

Harin Boko Haram a Najeriya
Image caption Harin Boko Haram a Najeriya

Algeria ta ce, kungiyar Jama'atu Ahlil Sunnah lidawati waal jihad ta Najeriya, wadda aka fi sani da Boko Haram, ta na da alaka da kungiyar Al Qaeda a yankin Maghreb.

Mataimakin Ministan harkokin wajen Algeria, Abdulkader Messahel, wanda ya bayyana hakan, ya ce kasar na da bayanan sirrin dake nuni da cewa, akwai taimakon da kungiyar Al Qaeda take baiwa Boko Haram a Najeriya.

An dai jima ana hasashen cewa kungiyar Boko Haram na samun taimako daga wasu kungiyoyin waje.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce, kawo yanzu ba ta sami bayyanan da ke nuna cewa akwai dangantaka tsakanin Boko Haram da Al Qaeda ba.

Mataimakin ministan harkokin wajen Algeriar ya ce za a shirya wani taro tare da jami'an Najeriya a kasar Mauritania, kan yadda za'a magance bunkasar Al Qaeda a yankin.

Karin bayani