Sabuwar zanga-zanga a Masar bayan sallar Juma'a

Masu zanga-zanga a dandalin Tahrir Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga a Kasar Masar na sake shirin taruwa a dandalin Tahrir bayan sallar Juma'ah

Masu zanga-zanga don ganin bayan mulkin soji a Masar na fatan dimbin mutane za su garzaya Dandalin Tahrir da ke birnin Alkahira bayan sallar Juma'a.

Mutane masu dimbin yawa sun ci gaba da kasancewa a Dandalin duk kuwa da rahotannin da kafofin yada labaran gwamnati suka bayar cewa wani tsohon Firayim Ministan Kasar, Kamal Ganzouri, ya amince ya kafa sabuwar gwamnati, bayan wata tattaunawa da ya yi da majalisar mulkin sojin Kasar.

Masu aiko da rahotanni sun ce yanzu shekarun Mista Ganzouri saba'in da takwas da haihuwa kuma zai yi wuya ya burge matasan da ke zanga-zangar neman kawo karshen mulkin sojin.

Sai dai daya daga cikin masu zanga-zangar ya fadawa BBC cewa ya gamsu da nadin Kamal Al-Ganzouri, kuma yana masa fatan alheri.

Karin bayani