Kasuwannin kudade sun dan farfado

Praministan Italiya Mario Monti Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Praministan Italiya Mario Monti

Kasuwannin hannayen jari sun nuna alamun farfadowa, bayan nada Mario Monti a matsayin Praministan rikon kwarya na kasar Italiya.

A jiya ne aka bukaci Mr Monti, wanda masanin tattalin arzikin kasa ne, kuma tsohon kwamishinan tarayyar Turai, da ya kafa sabuwar gwamnati wadda zata ceto kasar daga kangin bashin da ta afka.

Gwamnatin dai ta yi nasarar karbar bashin Euro biliyan 3, a lokacin baje kolin basusuka na baya baya.

Sai dai ana ganin cewa an tsawwala ma ta kudin ruwa.

A makon jiya darajar hannayen jari a kasashen Turai ta yi kasa.

Karin bayani