Tattalin arzikin Japan ya soma farfadowa

Fira Ministan kasar japan Yoshihiko Noda Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tattalin arzikin kasar Japan ya soma farfadowa bayan koma bayan daya samu sakamakon bala'in girgizar kasar data lalata kamfanonin kasar

Tattalin arzikin Japan ya bunkasa da kashi shida cikin dari a rubu'in da ya fara daga watan Yuli zuwa watan Satumba na bana, bayan koma bayan da gigizar kasa da kuma bala'in tsunami suka haifar a watan Maris.

Wannan ne dai karo na farko tun bayan bala'o'in biyu da tattalin arzikin kasar ta Japan ya yi irin wannan bunkasa a rubu'in shekara.

Masana dai sun bayyana cewa farfadowar kasuwancin fita da kayayyaki waje da kuma hadahada a cikin gida ita ce ta haddasa bunkasar tattalin arzikin.

Girgizar kasa da kuma bala'in tsunami daya afkawa kasar a watan Maris dai sun lalata masana'antu a arewa maso gabacin kasar, inda suka girgiza kayayyakin da kamfanonin dake samar da kayan lataroni da kuma motoci ke samarwa, amma sai dai tattalin arzikin kasar ya farfado nan da nan.

Daya daga cikin dalilan da suka sa haka shine yadda aka samu bunkasar sayar da kayayyakin wutar lantarki da kuma yadda jama'a suke ta kokarin ririta wutar lantarkin da suke samu duk da illar da girgizar kasar ta yiwa tashar Fukushima

Amma masana tattalin arziki na gargadin cewar ba lallai bane bunkasar tattalin arzikin Japan din ya dore

Rikicin dake faruwa a nahiyar turai na basusuuka ya taimaka wajen daga kudin Yen sama a 'yan makonnin nan, abinda yasa dole saida gwamnati ta shigo cikin hada hadar kasuwar kudaden kasar

Sai kuma ambaliyar ruwan Thaliland data lalata kamfanonin kasar Japan din da dama dake da masana'antu a can

Karin bayani