An tsaurara matakan tsaro a Kabul saboda taron Jirga

Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Za a gudanar da taron Loya Jirga a kasar Afghanistan karkashin tsauraran matakan tsaro

Dakarun tsaro sun yi shirin ko-ta-kwana a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, inda dattawa da shugabannin al'umma su kusan dubu biyu suka taru don tattauna makomar kasar.

Shugaba Hamid Karzai ne dai ya kira taron na Loya Jirga don tattaunawa a kan batun sasantawa da masu tayar da kayar baya da kuma yiwuwar kulla kawance ta fuskar tsaro tsakanin kasar ta Afghanistan da Amurka.

Kungiyar Taliban dai ta ce za ta kai hari inda za a gudanar da taron.

Wasu masu lura da al'amuran siyasar kasar dai na ganin cewar taron ba shi da wata fa'ida, kuma wata dama ce da Shugaba Karzai yake son ya yi amfani da ita wajen sauya kundin tsarin mulkin kasar.

Karin bayani