'Za mu daukaka kara' -Dakingari

Gwamna Sa'idu Dakingari na jahar Kebbi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan shine zaben Gwamna na farko da aka soke a matakin kotunan sauraron kararrakin zabe

Gwamna Sa'idu Usman Dakingari ta bakin lauyansa Barista Samson Egege ya ce bai gamsu da hukuncin kotun kararrakin zabe da ya soke zabensa a matsayin gwamnan jahar Kebbi ba.

Lawyan ya shaida wa BBC cewar 'kotu dai ta yanke hukuncin ta, amma ba mu amince da shi ba'.

Ya kara da cewar 'muna da namu korafe-Korafen kuma Alhamdulillahi akwai damar daukaka kara, don haka yanzu muna jiran umarni na gaba daga wadanda muke baiwa kariya, amma tabbas zamu daukaka kara kan wannan hukuncin'.

Su kuwa Lauyoyin jam’iyyar adawa sun ce sun yi maraba da hukuncin kamar yadda daya daga cikinsu, Barista Chima Okereke ya shaida wa BBC.

Shi ma dan takarar gwamnan na Jam’iyyar ta CPC Alhaji Abubakar Malam ya kira wani taron manema labarai bayan sanar da hukuncin, inda ya bayyana cewar ya karbi hukuncin ne da zuciya biyu.

Wannan dai ya kasance zaben Gwamna na farko da aka soke a matakin kotunan sauraron kararrakin zabe tun bayan kafa su a watan Mayu kuma ga alama shi ne na karshe kasancewar wa’adin da aka deba musu ya kawo karshe.

Karin bayani