Mutane sun hallaka a arewa maso gabacin Kasar Kenya

Taswirar Kasar Kenya Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Jerin fashe-fashe a arewa maso gabashin Kasar Kenya ya haddasa mutuwar mutane.

Wasu jerin fashe-fashe a arewa maso gabashin Kenya ya haddasa mutuwar akalla mutane hudu, yayin da wasu fiye da talatin kuma suka jikkata.

Akasarin wadanda abin ya shafa dai farar hula ne mazauna garin Garissa, mai tazarar kilomita kusan dari daga kan iyakar Kasar da Somalia.

Tun da farko dai wani bom da ya fashe a gefen titi ya hallaka soja daya, ya kuma raunata wasu sojojin guda hudu a garin Mandera da ke kan iyaka.

A watan jiya ne dai Kenya ta tura sojojinta cikin Somalia domin su yaki kungiyar masu tsattsauran ra'ayin Islama ta Al-Shabaab.

Karin bayani