'Italiya na bukatar kasancewa kakkarfar kasa' Mario Monti

Mario Monti, Sabon Fira Ministan kasar Italiya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sabon Fira Ministan kasar Italiya na fuskantar kalubalen sake farfado da tattalin arzikin kasar

Sabon Fira Ministan da aka nada a kasar Italiya, Mista Mario Monti, ya ce kasar Italiyan na bukatar kasancewa kakkarfar kasa wacce za a dogara da ita a Turai ba kasa mai rauni ba.

Mista Monti, wanda ke yunkurin kafa majalisar ministoci, zai fuskanci kalubalansa na farko ne yau Litinin yayin cinikin takardun lamuni na gwamnatin Italiya.

Yawan kudin ruwan da takardun lamunin za su jawo ne dai zai nuna ko kasuwannin hada-hadar kudade na da kwarin gwiwa cewa Mista Monti zai iya ceto kasar daga tarkon bashi.

Mista Monti yace zai tunkari matsalolin kasar ba tare da wani bata lokaci ba. Kuma a wani jawabi da ya yi a baya-bayan nan Mista Monti yace zai mikawa majalisar dokokin kasar Italiyan wasu matakan tsuke bakin aljihu wadanda ba lallai bane jama'ar kasar su so.

Cikin matakan farfado da tattalin arzikin kasar da ake jin cewar zai gabatarwa 'yan majalisar kasar sun hada da sanya haraji akan masu ajiyar kudade a banki.

An dai tilasatawa tsohon Fira Ministan kasar, Silvio Berlusconi, ya yi murabus ne bayan kudin ruwan ya haura kashi bakwai cikin dari.

Sai dai Mista Berlusconi ya bayyana a talabijin yana kare gwamnatinsa inda yace 'an wajabta mana fuskantar wannan matsala wadda ba a Italiya ta samo asali ba, ba kuma yawan basussukan mu ne ya haifar da ita ba'.

Karin bayani