Karanci abinci a Nijar

wasu mata manoma a Nijar Hakkin mallakar hoto b
Image caption wasu mata manoma a Nijar

A jamhuriyar Nijar maganar karancin abincin da ake jin kasar za ta fuskanta a bana sakamakon rashin kyawon damunar ta bana na ci gaba da jan hankalin bangarori daban daban na al'umar kasar.

Bayan kungiyoyin kare hakin dan adam,da ita kanta gwamnati da suka nuna fargabansu tare da yin kira ga kasashen duniya su taimaka, a yanzu yan majalisar dokokin kasar ne suka yi bitar matsalolin da kasawar damunar ka iya haddasawa.

'Yan majalisar dokokin sun ce akwai kuskure a rahoton da gwamnati ta bayar game da batun abincin da aka samu bana inda ta ce a wasu yankuna da suka hada da Maradi da kuma Dosso, yawan abincin da aka samu ya zarta ma bukatun mazaunan wadannan yankuna.

'Yan majalisar sun kuma yi kira ga gwamnati da ta dauki matakan gaggawa domin shawo kan wannan matsala.

Karin bayani