'Yan sanda sun rufe sansanin Oakland a Amurka

Sansanin Oakland a Amurka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sanda sun tsare wasu daga cikin masu zanga zangar da suka taru a birnin Oakland dake kasar Amurka

'Yan sanda a Jihar California ta Amurka sun rufe daya daga cikin sansanonin masu adawa da rashin daidato irin na tsarin jari-hujja wadanda suka bazu a kasar.

Jim kadan bayan ketowar alfijir ne dai 'yan sandan suka fara kawar da mutanen da ke cikin tantuna a sansanin Oakland.

'Yan sandan sun kama mutane fiye da talatin.

'Yan sandan sun rinka ciccire bajon dake jikinsu domin gudun kada a gane su.

An kuma hana 'yan jarida tafiya cikin tantunan da aka kakkafa.

Rahotanni sun ce an tsare mutane da dama amma ba a samu rahotan barkewar wani tashin hankali ba.

Masu zanga- zangar wadanda suka shirya gudanar da ita cikin lumana sun yi ta rera wakoki kuma suna fadin cewar kamen ba zai dakatar da su ba

Magajiyar garin Oakland, Jean Quan ta ce dole ne su rufe sansanin saboda tashe- tashen hankulan dake aukuwa.

Karin bayani