An harbe mutane biyu a Kasar Saudiyya

Sarki Abdallah na Saudi Arabiya
Image caption Hukumomi a Saudiyya sun ce jami'an tsaro sun yi musayar wuta da wasu 'yan bindiga a wannan makon

Hukumomi a Saudi Arabia sun ce an bindige mutane biyu a rikici na baya-bayan nan da ya barke a gabashin kasar.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce jami'an tsaro sun yi musayar wuta da wasu 'yan bindiga yayin wata jana'iza a farkon wannan makon.

Ko a watan jiya ma rahotanni sun ce mutane goma sha hudu sun jikkata a lokacin wata zanga-zanga a yankin, inda nan ne cibiyar 'yan shi'a marasa rinjaye a kasar.

Hukumomin sun ce 'yan bindigar na aiki ne ga wata Kasar waje.

Karin bayani