BBC navigation

An harbe mutane biyu a Kasar Saudiyya

An sabunta: 24 ga Nuwamba, 2011 - An wallafa a 06:03 GMT
Sarki Abdallah na Saudi Arabiya

Hukumomi a Saudiyya sun ce jami'an tsaro sun yi musayar wuta da wasu 'yan bindiga a wannan makon

Hukumomi a Saudi Arabia sun ce an bindige mutane biyu a rikici na baya-bayan nan da ya barke a gabashin kasar.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce jami'an tsaro sun yi musayar wuta da wasu 'yan bindiga yayin wata jana'iza a farkon wannan makon.

Ko a watan jiya ma rahotanni sun ce mutane goma sha hudu sun jikkata a lokacin wata zanga-zanga a yankin, inda nan ne cibiyar 'yan shi'a marasa rinjaye a kasar.

Hukumomin sun ce 'yan bindigar na aiki ne ga wata Kasar waje.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.