Ya kamata shugaba Assad yayi murabus

Bashar al-Assad Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bashar al-Assad

Sarki Abdullah na Jordan ya gaya wa BBC cewa, ya kamata shugaban Syria, Bashar al-Assad yayi murabus, domin kare mutuncin kasarsa.

Sarkin ya ce, rikicin da ake fama da shi a kasar Syriar ya zama babbar matsala, kuma yana janyo damuwa a dukan kasashen yankin.

Sarki Abdullah ya ce, ana iya warware rikicin ta hanyar yin sauye-sauyen siyasa masu yawa.

Tun lokacin da gwamnatin Syria ta soma murkushe 'yan adawa masu zanga zanga a kasar, wannan ne karon farko da wani shugaban Larabawa ya fito fili yayi kira ga shugaba Assad da ya sauka daga mulki.

Tun farko dai ministan harkokin wajen Syria, Walid al-Moualem, ya maida martani mai nuna rashin saduda, game da dakatar da kasar daga cikin kungiyar kasashen Larabawa.

Ya ce, Syria ba zata sunkuyo ba, kuma makarkashiyar da ake shirya mata ba za ta yi nasara ba.

Karin bayani